Shugaban Chadi, Idris Deby ya rasu

Shugaban Chadi, Idris Deby ya rasu
Share This:

Shugaban Chadi, Idris Deby ya rasu

Rahotanni daga ƙasar Chadi sun tabbatar da rasuwar Shugaban Ƙasar, Idris Deby Itno, mai shekaru 68.

Bayanan sojojin ƙasar sun nuna marigayin ya kwanta dama ne sakamakon raunukan da ya samu a karawar da ya jagoranci dakarunsu wajen fatattakar ‘yan tawayen FACT na ƙasar.

Bayanan sosjojin sun sake nuna cewa, marigayi Deby ya rasu ne jim kaɗan bayan sanar da nasarar da ya samu a babban zaɓen ƙasar da aka gudanar a ranar 11, Afrilu, 2021.

A cewar Hukumar Zaɓen Chadi, marigayin ya lashe zaɓen ne da kashi 79.32 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa.

Shugaban Chadi, Idris Deby ya rasu
Shugaban Chadi, Idris Deby ya rasu

Sanarwa ta daban da Rundunar Sojin Chadin ta bayar ta nuna ɗan marigayin, Deby Janar Mahammat Deby, shi ne za a naɗa a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin riƙon ƙwaryar Soji.

READ:  TODA Cultural Carnival Will Strengthen More Unity Across Diverse Culture - Says Barrister Magaji

Marigayi Deby ya shafe shekaru 31yana mulkin ƙasar kafin cim ma ajalinsa a wannan Talatar.

Nasarawa za ta gabatar da garambawul a kan kasa don kawar da matsalolin daga sauƙin yin kasuwanci

Kasancewar Chadi a matsayin ƙasa mafi ƙarfi a yaƙin da ake yi da Boko Haram a yankin tafkin Chadi, mutuwar shugaban ka iya zama koma baya a ƙoƙarin da ake yi na daƙile ta’addancin da ya addabi ƙasashen da ke maƙwabtaka da ƙasar.

Share This:

Leave a Reply